Wednesday, 24 August 2016
Wasu ‘yan bindiga da har zuwa yanzu ba a san ko su wanene ba sun sace Honarabul Ibrahim Ismail Dan Majalisar Jihar Kaduna mai Wakiktar Tudun Wada. An dai sace Dan majalisar ne a safiyar jiya Talata, inda masu garkuwan sukai awan gaba da shi akan hanyarsa don ziyartar dan uwansa a yankin Abakwa. Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Kaduna Aliyu Usman ya tabbatar da aukuwar lamarin yayin da ya bayyanawa manema labarai cewa, yanzu haka hukumar na bnciken lamarin.
Hukumar ‘yan sandan jihar Ogun sun cigaba da tsare Joe Fortomose Chinakwe wanda ya sanyawa karensa suna Buhari a kurkuku.
Rundunar ‘yan sandan jihar ce dai ta gurfanar da Joe Fortomose Chinakwe a gaban kotun majistare a jiya Litinin, bisa zargin shirin tada zaune tsaye, sakamakon yawon da yake yi da karen sa, wanda ya rubuta sunan Buhari a sassan jikin karen.
Jim kadan, kotun dai ta bada belinsa, to sai dai bai cika sharudan beli ba, dan haka aka ci gaba da tsare shi a gidan kaso.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment