Wednesday, 24 August 2016
CBN Ta Dakatar Da Bankuna Tara Daga Hada-Hadar Kudaden Waje
Babban bankin Najeriya, CBN ya dakatar da wasu bankuna tara hada-hada da kudaden kasashen waje saboda kin sanya fiye da dala biliyan biyu na kamfanin mai na kasar, a asusun bai daya na gwamnati kamar yadda aka tsara.
Sai dai Babban bankin Najeriya, CBN bai fito a hukumance ya bayyana hakan ba, amma an dauki matakin ne bayan korafin da kamfanin na NNPC ya kai ga gwamnatin tarayya.
Bayanai sun nuna cewa sabon shugaban NNPC, Dokta Maikanti Kacalla Baru ya bukaci gwamnatin ta taimaka wajen ganin bankunan sun sanya kudaden a lalitar gwamnati.
Bankunan da lamarin ya shafa sun hada da: First Bank, UBA, First City Monument Bank, Diamond Bank, Fidelity Bank, Heritage Bank, Sterling Bank, Key stone Bank da kuma Sky Bank.
Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta bullo da tsarin asusun bai daya, wadda dukkan hukumomi da ma’aikatun gwamnati za su dinga zuba kudade.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment