Wednesday, 24 August 2016

Wasu ‘yan bindiga da har zuwa yanzu ba a san ko su wanene ba sun sace Honarabul Ibrahim Ismail Dan Majalisar Jihar Kaduna mai Wakiktar Tudun Wada. An dai sace Dan majalisar ne a safiyar jiya Talata, inda masu garkuwan sukai awan gaba da shi akan hanyarsa don ziyartar dan uwansa a yankin Abakwa. Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Kaduna Aliyu Usman ya tabbatar da aukuwar lamarin yayin da ya bayyanawa manema labarai cewa, yanzu haka hukumar na bnciken lamarin.







Hukumar ‘yan sandan  jihar Ogun sun cigaba da tsare Joe Fortomose Chinakwe wanda ya sanyawa karensa suna Buhari a kurkuku.

Rundunar ‘yan sandan jihar ce dai ta gurfanar da Joe Fortomose Chinakwe a gaban kotun majistare a jiya Litinin, bisa zargin shirin tada zaune tsaye, sakamakon yawon da yake yi da karen sa, wanda ya rubuta sunan Buhari a sassan jikin karen.

Jim kadan, kotun dai ta bada belinsa, to sai dai bai cika sharudan beli ba, dan haka aka ci gaba da tsare shi a gidan kaso.

Yan Bindiga Sun Sace Wani Dan Majalisar Jihar Kaduna








Wasu ‘yan bindiga da har zuwa yanzu ba a san ko su wanene ba sun sace Honarabul Ibrahim Ismail Dan Majalisar Jihar Kaduna mai Wakiktar Tudun Wada.

An dai sace Dan majalisar ne a safiyar jiya Talata, inda masu garkuwan sukai awan gaba da shi akan hanyarsa don ziyartar dan uwansa a yankin Abakwa.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Kaduna Aliyu Usman ya tabbatar da aukuwar lamarin yayin da ya bayyanawa manema labarai cewa, yanzu haka hukumar na bnciken lamarin.

CBN Ta Dakatar Da Bankuna Tara Daga Hada-Hadar Kudaden Waje








Babban bankin Najeriya, CBN ya dakatar da wasu bankuna tara hada-hada da kudaden kasashen waje saboda kin sanya fiye da dala biliyan biyu na kamfanin mai na kasar, a asusun bai daya na gwamnati kamar yadda aka tsara.

Sai dai Babban bankin Najeriya, CBN bai fito a hukumance ya bayyana hakan ba, amma an dauki matakin ne bayan korafin da kamfanin na NNPC ya kai ga gwamnatin tarayya.

Bayanai sun nuna cewa sabon shugaban NNPC, Dokta Maikanti Kacalla Baru ya bukaci gwamnatin ta taimaka wajen ganin bankunan sun sanya kudaden a lalitar gwamnati.

Bankunan da lamarin ya shafa sun hada da: First Bank, UBA, First City Monument Bank, Diamond Bank, Fidelity Bank, Heritage Bank, Sterling Bank, Key stone Bank da kuma Sky Bank.

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta bullo da tsarin asusun bai daya, wadda dukkan hukumomi da ma’aikatun gwamnati za su dinga zuba kudade.

Sunday, 21 August 2016

SAI YANZU NA GANE DALILIN RUFE BODA Daga Shafin Auwal G. Danborno






SAI YANZU NA GANE DALILIN RUFE BODA
Daga Shafin Auwal G. Danborno
Da za a yi hakuri a rufe bodar nan, tsawon shekaru goma ko fiye da arziki ya wadata. Dan rufe bodar nan da aka yi ya sanya da yawan mutane bana sun yanki daji sun fara noma.
Wasu ma kamar ni ba mu San cewa muna da Gonaki da Muka gada a wajen kakanni ba. Haba jama'a duk mutanen kauye sun zo birni Sun tare ba tare da wata ingantacciyar sanaa ba. Sai ka ga garjejen kato yana tallar raken da bai fi na Nera dari biyu ba duk jarin, ko yankan farce dss. Duk sun baro gonakansu ciyawa ta cika su.
Yanzu da suka ga abin ya ci uwar mai shayi kowa ya Koma gida. Tun kaka ba ta shigo ba har abinci ya fara saukowa duk da cewa wannan shekarar ba wani tallafi daga gwamnati. Tabbas shekara mai zuwa muna sanya rai shinkafa za ta dawo dari biyu kwano daya duk kyan ta.


Saturday, 20 August 2016

Dan Wasan Jamaica Bolt Ya Ci Zinare Na Uku A Gasar Olympic






Daga Ahmadu Manager Bauchi.

Dan wasan tseren Jamaica Usain Bolt ya jagoranci tawagar kasar, a tseren mutum hudu na mita dari a gasar wasannin Olympics da ake gab da kammalawa a birnin Rio na Brazil.

Usain Bolt ya samu nasarar cin zinare a tseren da suka yi, inda ya tsallake layi na karshe cikin wani sabon salo da ya bashi damar tserewa dan wasan Japan wanda ya ci azurfa.

Wannan nasara ta sanya Bolt ya samu zinare na uku a wasannin da ya yi.

Bayan kammala wasan Usain Bolt ya burge 'yan kallo da masu daukar hoto, inda ya karkacewa da irin salon daukar hoto da aka san shi da shi.

Ya kuma fadi irin farin cikin da ya ke ciki da alfahari da kan shi kan nasarar da ya yi.

A halin yanzu dai shi ke rike da kambun tseren mita dari, da na mita dari biyu na Olympics tun fiye da shekaru goma.