Thursday, 13 October 2016

Gwamnatin Tarayya Ta Tabbatar Da Sakin 21 Daga Cikin 'Yan Matan Chibok





Gwamnatin Tarayya Ta Tabbatar Da Sakin 21 Daga Cikin 'Yan Matan Chibok

Ga Abinda Kakakin Shugaban Kasa Malam Garba Shehu Ya Ce:

"Ta tabbata an saki 21 daga cikin 'yan matan Chibok kuma yanzu haka suna tare da hukumar DSS.

"A dazun nan Babban Daraktan hukumar ta DSS Malam Lawal Daura ya gama yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari bayani kan batun.

"Sako yaran ba ya rasa na saba da tattaunawar da gwamnatin tarayya take da kungiyar Boko Haram din da taimakon kingiyar agaji ta duniya da kuma gwamnatin kasar Switzaland. Kuma za a ci gaba da tattaunawar.

Shugaban kasa ya ji dadin sakin yaran.

Yanzu haka shugaban DSS, Malam Lawal Daura yana bukatar yaran su samu hutu sabida sun gaji, kafin daga bisani a mika su ga mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo. Saboda shugaba Buhari zai haura kasar Jamus an jima.

Za a kuma a bayyana sunayen wadanda aka sako din nan bada jimawa ba.




Wednesday, 24 August 2016

Wasu ‘yan bindiga da har zuwa yanzu ba a san ko su wanene ba sun sace Honarabul Ibrahim Ismail Dan Majalisar Jihar Kaduna mai Wakiktar Tudun Wada. An dai sace Dan majalisar ne a safiyar jiya Talata, inda masu garkuwan sukai awan gaba da shi akan hanyarsa don ziyartar dan uwansa a yankin Abakwa. Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Kaduna Aliyu Usman ya tabbatar da aukuwar lamarin yayin da ya bayyanawa manema labarai cewa, yanzu haka hukumar na bnciken lamarin.







Hukumar ‘yan sandan  jihar Ogun sun cigaba da tsare Joe Fortomose Chinakwe wanda ya sanyawa karensa suna Buhari a kurkuku.

Rundunar ‘yan sandan jihar ce dai ta gurfanar da Joe Fortomose Chinakwe a gaban kotun majistare a jiya Litinin, bisa zargin shirin tada zaune tsaye, sakamakon yawon da yake yi da karen sa, wanda ya rubuta sunan Buhari a sassan jikin karen.

Jim kadan, kotun dai ta bada belinsa, to sai dai bai cika sharudan beli ba, dan haka aka ci gaba da tsare shi a gidan kaso.

Yan Bindiga Sun Sace Wani Dan Majalisar Jihar Kaduna








Wasu ‘yan bindiga da har zuwa yanzu ba a san ko su wanene ba sun sace Honarabul Ibrahim Ismail Dan Majalisar Jihar Kaduna mai Wakiktar Tudun Wada.

An dai sace Dan majalisar ne a safiyar jiya Talata, inda masu garkuwan sukai awan gaba da shi akan hanyarsa don ziyartar dan uwansa a yankin Abakwa.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Kaduna Aliyu Usman ya tabbatar da aukuwar lamarin yayin da ya bayyanawa manema labarai cewa, yanzu haka hukumar na bnciken lamarin.

CBN Ta Dakatar Da Bankuna Tara Daga Hada-Hadar Kudaden Waje








Babban bankin Najeriya, CBN ya dakatar da wasu bankuna tara hada-hada da kudaden kasashen waje saboda kin sanya fiye da dala biliyan biyu na kamfanin mai na kasar, a asusun bai daya na gwamnati kamar yadda aka tsara.

Sai dai Babban bankin Najeriya, CBN bai fito a hukumance ya bayyana hakan ba, amma an dauki matakin ne bayan korafin da kamfanin na NNPC ya kai ga gwamnatin tarayya.

Bayanai sun nuna cewa sabon shugaban NNPC, Dokta Maikanti Kacalla Baru ya bukaci gwamnatin ta taimaka wajen ganin bankunan sun sanya kudaden a lalitar gwamnati.

Bankunan da lamarin ya shafa sun hada da: First Bank, UBA, First City Monument Bank, Diamond Bank, Fidelity Bank, Heritage Bank, Sterling Bank, Key stone Bank da kuma Sky Bank.

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta bullo da tsarin asusun bai daya, wadda dukkan hukumomi da ma’aikatun gwamnati za su dinga zuba kudade.

Sunday, 21 August 2016

SAI YANZU NA GANE DALILIN RUFE BODA Daga Shafin Auwal G. Danborno






SAI YANZU NA GANE DALILIN RUFE BODA
Daga Shafin Auwal G. Danborno
Da za a yi hakuri a rufe bodar nan, tsawon shekaru goma ko fiye da arziki ya wadata. Dan rufe bodar nan da aka yi ya sanya da yawan mutane bana sun yanki daji sun fara noma.
Wasu ma kamar ni ba mu San cewa muna da Gonaki da Muka gada a wajen kakanni ba. Haba jama'a duk mutanen kauye sun zo birni Sun tare ba tare da wata ingantacciyar sanaa ba. Sai ka ga garjejen kato yana tallar raken da bai fi na Nera dari biyu ba duk jarin, ko yankan farce dss. Duk sun baro gonakansu ciyawa ta cika su.
Yanzu da suka ga abin ya ci uwar mai shayi kowa ya Koma gida. Tun kaka ba ta shigo ba har abinci ya fara saukowa duk da cewa wannan shekarar ba wani tallafi daga gwamnati. Tabbas shekara mai zuwa muna sanya rai shinkafa za ta dawo dari biyu kwano daya duk kyan ta.


Saturday, 20 August 2016

Dan Wasan Jamaica Bolt Ya Ci Zinare Na Uku A Gasar Olympic






Daga Ahmadu Manager Bauchi.

Dan wasan tseren Jamaica Usain Bolt ya jagoranci tawagar kasar, a tseren mutum hudu na mita dari a gasar wasannin Olympics da ake gab da kammalawa a birnin Rio na Brazil.

Usain Bolt ya samu nasarar cin zinare a tseren da suka yi, inda ya tsallake layi na karshe cikin wani sabon salo da ya bashi damar tserewa dan wasan Japan wanda ya ci azurfa.

Wannan nasara ta sanya Bolt ya samu zinare na uku a wasannin da ya yi.

Bayan kammala wasan Usain Bolt ya burge 'yan kallo da masu daukar hoto, inda ya karkacewa da irin salon daukar hoto da aka san shi da shi.

Ya kuma fadi irin farin cikin da ya ke ciki da alfahari da kan shi kan nasarar da ya yi.

A halin yanzu dai shi ke rike da kambun tseren mita dari, da na mita dari biyu na Olympics tun fiye da shekaru goma.




Thursday, 28 July 2016

Ina Sane Da Halin Kuncin Da Talakawan Kasar Nan Ke Ciki, Inji Shugaba Buhari





Shugaban kasa Mummadu Buhari yace gwamnatinsa na sane da matsalolin da talakawan kasar nan ke fuskanta sannan ya yi kira ga shugabannin addinin Musulunci su kaiwa jama’a sakon bege mai kyau cewa lamura zasu daidaita.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a yayin taron da ya yi da majalisar limaman Abuja a fadarsa a yau Alhamis, innda ya bukaci limaman addini da su dinga kwantar da hankulan jama’arsu a duk fadin kasar. Yace shugabancin kasar, a mataki daban daban, na kokarin warware matsalolin talauci da rashin aikin yi da na tsaro da suka addabi kasar.

Yace gwamnati ta baiwa aikin noma fifiko domin kirkiro ayyukan yi wa miliyoyin ‘yan kasar da kuma baiwa kasar damar ciyar da kanta ba tare da tsoron yunwa ba. Kodayake an soma kokari gadan gadan akwai babban shirin samarda taki da maganin kashe kwari da kuma shiri ma daminar badi.

Domin kowa ya ci muradun wannan shirin shugaban yace an bukaci gwamnatocin jihohi da shugabannin al’umma, a duk fadin kasar, su yi kungiyoyin hadin kai na taimakan juna ko cooperatives tare da nanata cewa taimako irin na dabaru da kayan aiki za’a ba mutane ba kudi ba.

Shugaban ya kuma shaidawa shugabannin addinin kokarin da gwamnatinsa keyi domin inganta wutar lantarki a kasar. Saboda haka ne ma kasar zata kawo wadanda zasu saka jari a harkokin wutar lantarki daga kasar Sin da wasu kasashen da kasar ke abokantaka dasu da suke son saka jari a aikin wuta da za’a yi a Mambila da wasu wuraren.

Buhari ya tabbatar cewa matakan da gwamnatinsa take dauka a kan rikicin yankin Niger Delta zasu kaiga dawamammen zaman lafiya.

Dangane da yakin da ya keyi da cin hanci da rashawa da ‘yan ta’adan Boko Haram, Shugaba Buhari yace gwamnatinsa za ta dage, babu gudu babu ja da baya. “Bamu da niyyar tursasawa kowa ko cin mutuncin wani. Adalci da tabbatar da yakamata da ba kowa hakkinsa muka sa a gaba, inji Shugaba Buhari.

Ya sake jaddada cewa duk wanda aka samu ya saci kudin jama’a to za’a tilasta masa ya dawo dasu domin kasar na bukatar kudin.

Tun farko, a madadin sauran limaman, shugaban majalisar limaman dake Abuja Dr Tajudeen Muhammad Bello Adigun ya yaba da mulkin Buhari musamman yaki da cin hanci da rashawa da ‘yan Boko Haram. Kana ya jawo hankalin shugaban kan tattalin arzikin kasar, da matsalar kiwon lafiya da Rashin aikin yi.