Gwamnatin Tarayya Ta Tabbatar Da Sakin 21 Daga Cikin 'Yan Matan Chibok
Ga Abinda Kakakin Shugaban Kasa Malam Garba Shehu Ya Ce:
"Ta tabbata an saki 21 daga cikin 'yan matan Chibok kuma yanzu haka suna tare da hukumar DSS.
"A dazun nan Babban Daraktan hukumar ta DSS Malam Lawal Daura ya gama yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari bayani kan batun.
"Sako yaran ba ya rasa na saba da tattaunawar da gwamnatin tarayya take da kungiyar Boko Haram din da taimakon kingiyar agaji ta duniya da kuma gwamnatin kasar Switzaland. Kuma za a ci gaba da tattaunawar.
Shugaban kasa ya ji dadin sakin yaran.
Yanzu haka shugaban DSS, Malam Lawal Daura yana bukatar yaran su samu hutu sabida sun gaji, kafin daga bisani a mika su ga mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo. Saboda shugaba Buhari zai haura kasar Jamus an jima.
Za a kuma a bayyana sunayen wadanda aka sako din nan bada jimawa ba.